Lyrics

LYRICS: Hamisu Breaker – Masoyana

Hamisu breaker masoya

kukan kurciya jawabine mai hankali zai gane haka hikimar zance ne na dan hausa gwanin saka

Ya Allah ka kareni daga harshe mai rauni tsarkake mini duk tunani ni mai koyar waka

nazo gaida masoyana dan ni wasu Sun sauya yau suna gane murya suka ce mini Mai Waka.

duk ina jin sakonni naku domin gaidani wasu ma zasu kirani ina jin dadin haka

Allah mai ikone yau dae ni bako ne kamar yau zan zama dan gari kar ku kirani gwanin waka

ma, abota sauraro dan ku yau na tsaro baitoti na kwararo muku kuyi mini sanbarka.

na gaida masoyana masu kewar zancena nima ga sakona a gareku kamar haka.

hakuri Alkairi ne ladabi kuma riba ne mu taimaka wa iyayenmu makasudin nasararmu

hassada kada muyi kyashi ganin ido ko Alwashi na cin mutuncin mai bashi mu tallafawa yara kanana

kada muyi sata kunji yan uwa son zuciya mu gina ganuwa Don itace ke tsaka renuwa kar ka yada Abokanka

Lokaci zai sauka kamar ruwa muyi duba fannin rayuwa ilimi ne jigo yan uwa

roki Allahu ya baka roki Allahu ya baka mu roki Allahu ya bamu

ki roki Allahu ya baki na roki Allahu ya bani.

Rubutawa :-

L Smart Bello

Download Mp3

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.