Lukaku Zai Maye Gurbin Cavani Na PSG

0 4,367

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta shiga sahun kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan wajen neman dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Rumelu Lukaku a kakar wasa mai kamawa domin ya maye gurbin Cavani.

Lukaku dai yana daya daga cikin ‘yan wasan ake saran zasuyi kasuwa a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa bayan da a kwanakin baya ya bayyana cewa yana fatan watarana zai koma kasar Italiya da buga wasa.

Har ila yau, wasu rahotanni daga kasar Italiya dai sun tabbatar da cewa tuni Antonio Conte, wanda ake tunanin zai zama kociyan Inter Milan a karshen kakar wasa ya amince da karbar aikin koyar da kungiyar kuma yayi Magana da Lukaku akan komawa Inter Milan din.

Rahotannin kuma suka bayyana cewa Inter Milan tayi alkawarin zata bawa Conte kudi a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasan da za’a bude domin siyan ‘yan wasa wadanda zasu taimaka masa a kakar wasa mai zuwa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 55

Sai dai kungiyar kwallon ta PSG itama ta shiga zawarcin dan wasan wanda ya buga wasanni bakwai a karshen wasannin firimiya na bana batare daya zura kwallo a raga ba kuma kociyan kungiyar ya bayyana cewa zai iya rabuwa da dan wasan.

Har yanzu dai dan wasa Lukaku, dan kasar Belgium, yana da ragowar kwantaragin shekara uku a United kuma a kakar wasansa ta farko a kungiyar ya zura kwallaye 27 bayan ya koma United din daga Eberton . A kwanakin baya dai wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata yarda ta siyarwa da PSG Lukaku idan har zata siyar mata da dan wasa Edinson Cavani wanda shima yakeson barin kungiyar saboda rikicin da yake tsakaninsa da kociyan kungiyar.

#Hausaleadership

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: