Romelu Lukaku ya ce yana kafa sabon tarihi na kashin kansa a Manchester United.
Dan kwallon na kasar Belgium mai shekara 24, ya koma United ne kan kudi fan miliyan 75 bayan ya zura kwallo 25 a gasar Firimiya a Everton a kakar da ta gabata.
Lukaku, wanda shi ne dan wasan kasar waje na farko da ya zura kwallo 80 a Firimiya kafin ya cika shekara 24, ya ce: “ba zan iya cewa burina ya cika ba tukunna.
“Akwai sauran aiki a gabanmu, kuma in farin ciki da hakan, domin yana nufin cewa zan kara gogewa fiye da yadda na ke.”
Add Comment