Labarai

Lokaci Ya Yi Da Ya Kamata A Soke Lefe, Cewar Sheikh Bn Uthman

Daga Suleiman Abba (TBABA)

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Bn Uthman, ya bayyana cewar lokaci ya yi da ya kamata a soke yin lefe a kasar Hausa idan za a yi aure.

Malamin ya bayyana haka ne cikin wata shimfidar cigaba da karatun tafsiri da ya yi jiya Juma’a a masallacin Sahaba da ke unguwar Kundila a jihar Kano.

“Idan ka tashi neman aure, sai an bijiro maka da buƙatu iri-iri. Tin da na ambaci aure, lokaci ya yi da ya kamata hatta duk lefennan duk ku soke su.”

Wasu daga cikin mahalarta karatun da aka jiyo muryoyinsu sun yi saurin amsa wa da ‘Na’am, Lallai, Allah Ya sa, Amin Ya Allah (da babbar murya).

Sheikh Bn Uthman ya cigaba da cewa; “Ku fadamin wa ya ce a yi(lefe)? Mu muka jangwalo wa kanmu fitina da yawa. Ka haifi yarinya, ka yi mata tarbiya sannan ka sake yi mata gado ka kai, in ya(miji) ga dama ya koro maka ita, ka zo kana ta tagumi da sallallami.”

Malamin ya kafa hujja da aya ta hudu a cikin surah Nisa, in da ya ce Allah bai ce a yi wa mata lefeba.

Sai dai malamin ya ce ba yana inkarin al’ada bane, sai dai kar alada ta shigo da wahalarwa, in da ya ce tana saka mutane shiga cikin damuwar da ta ke sanya su siyar da kadarorinsu.

A gefe guda, malamin ya ce duk namijin da zai auri mace, shi ma ya kamata ya ɗauki ɗawainiyar gida, kayan ɗaki da kayan amfanin gida baki daya domin a cewarsa matar ya aura ba kayan ba.

Ya ƙara da cewa duk namijin da aka kawo masa kaya kadai babu mata, zai ce ba ya so.

“Kai da za ka auro ta, ka nemo gida ko naka ko na haya, siyo gadonka, siyo kayan ƙyaleƙyalenka, siyo kayan abincinka, komai kai za ka siyo gwargadon hali. Ke ki taso daga gidan iyayenki daga ke sai jakarki. Shin kayan ka ke aure ko matar, ka ƙaddara an kawo kayan amma babu matar, sai ka ce a kwashe kayan ba ka so.”

Batun kayan lefe da kayan daki dai ya dade ana tattaunashi tsakanin al’umma musamman a kafafen sadarwa, wasu na ganin kamatuwar sokewa, wasu na ganin dacewar cigaba da raya al’adar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: