-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Lauyoyi 18 Ne Zasu Kare Buhari A Shari`ar Atiku


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Turnuku fadin ibilisai, yaro bai gani ba balle ya raba, wannan shine kwatankwacin arangamar da za’a kwasa a gaban kotu tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar.

Majiyarmu ta ruwaito a ranar cewar Alhamis, 7 ga watan Maris ne aka fara zaman sauraron karar da Atiku ya shigar gaban kotun sauraron koken zaben shugaban kasa, inda yayi zargin INEC da APC sun shirya magudin da ya baiwa Buhari nasara a zaben shugaban kasa.

Sai dai wasu majiyoyi masu tushe sun ruwaito tuni shugaban kasa Buhari ya kammala tara wasu tawagar gogaggun lauyoyi da farfesoshin sharia da wasu masu take musu baya da adadinsu ya kai goma sha takwas da zasu tsaya tsayin daka don kare martabar nasarar da Buhari ya samu akan Atiku.

Jagoran tawagar lauyoyin nan shine

1. Cif Wole Olanipekun, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa mai lambar kwarewa ta SAN,

2. Kanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Akinola Osinbajo SAN,

3. kaakakin yakin neman zaben Buhari Festus Keyamo SAN.

4. Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, Abubakar Mahmoud SAN,

5. Femi Atoyebi SAN,

6. Mike Igbokwe SAN,

7. Niyi Akintola SAN,

8. Yusuf Ali SAN,

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

9. Osaro Egbobamien SAN,

10. Dakta Muiz Banire SAN,

11. Alex Iziyon SAN,

12. Banbella Anachebe SAN,

13. Charles Edosomwan SAN,

14. Funke Adekoya SAN.

15. Farfesa Taiwo Osipitan,

16. Ibrahim Bawa SAN,

17. Yakubu Maikyau,

Duba da jigogin shari’a dake cikin wannan tawaga, yasa ake ganin ba’a taba tara kwarrru, gogaggu kuma masana sharia a shari’ar shugaban kasa ba kamar wannan.

Shi jagoran ayarin lauyoyin, Wole Olanipekun sananne ne a harkar sharia, inda shine lauyan Buhari a karar da aka shigar dashi gaban kotu game da takardar shaidar kammala makarantar sakandari, kuma ya taba kare Tinubu a shekarar 2011 da aka shigar dashi kara gaban kotun da’ar ma’aikata.

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: