Kannywood

[Labari] Sabon Video Rahama Sadau Tare Da Mawaki ClassiQ ‘Kawai

Kalla Cikin Hotuna Yadda Tsohuwar Fitacciyar Jarumar Fina Finan Hausa Da Aka Kora Rahama Sadau Ta Sake Bayyana A Cikin Wani Sabon Faifan Video Tare Da Mawaki ClassiQ . Shin Ko Hakan Yana Nufin Cewa Jarumar Ta Samu Daukaka Kenan Fiye Da Yadda Take Ada 

Bisa La’akari Da Yadda Duniyar Mawaka Itace Kan Gaba Fiye Data Fina Finai A Wannan Lokaci.   Wanda Bisa La’akari Zamuga Cewa Dalilin Video Wakar Da Jaruma Rahama Sadau Tayi Na Farko Tare Da Mawaki ClassiQ Yayi Matukar Daga Darajar Ta.  Inda Fitaccen Mawaki Kuma Shahararre A Duniya ‘Akon Tare Da Shugan Dake Kula Da Fina Finan India Na Bollywood ‘Jeta Ameta Suka Gayyaceta Zuwa Kasar Amurka. Inda Har Ta Fara Samun Horo Na Musamman Akan Fina Finan Bollywood. Wanda Hakan Kuwa Dama Yana Daya Daga Cikin Kudurorin Da Jarumar Ta Dade Tana Wallafawa Musamman A Shafin Ta Na Intag Na Zama Word Actress Ba Kannywood Actress Ba Kadai. 

Wanda A Yanzu Haka Indai Har Kudurin Jarumar Ya Cika ta fara fitowa a Fina Finan Bollywood to tabbas nan bada jimawa ba babban kudurin ta na zama Word Actress  zai cika,  saka makon irin rawar data taka a masana antun shirya fina finai daban daban har Kala uku. 

1= Kannywood 
2= Nollywood
3= Bollywood 

Inda Yanzu Haka Aketa Yawo Da Tsegumin Cewa Jarumar Zata Fito A Wani Sabon Shirin Bollywood Mai Suna ‘The American King. 

KALLI SAURAN HOTUNANTA TARE DA CLASSIQ ‘KAWAI. 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.