Wasanni

La Liga: Barca da Real za su kara a Disamba

A cikin watan Disamba Real da Barca za su fafata a gasar La Liga

Hukumar da ke gudanar da La Ligar Spaniya ta fitar da jadawalin wasannin 2017/18, inda ta tsara Barcelona da Real Madrid za su buga El-Clasicon farko a watan Disamba.

Barcelona ce za ta fara ziyartar Bernabeu a ranar Laraba 20 ga watan Disamba a wasan mako na 17 a gasar.

 

Sai dai kuma watakila a sauya ranar fafatawar domin Real za ta buga gasar kofin zakarun kungiyoyin nahiyar duniya, domin za a yi wasan karshe a ranar 16 ga watan Disamba.

Ita kuwa Real za ta je Camp Nou a ranar Lahadi 6 ga watan Mayu a wasan mako na 36 a gasar ta La Liga.

Madrid mai rike da kofin La Liga, za ta fara wasan farko a kakar bana tsakanin 18 zuwa 21 ga watan Agusta, inda za ta ziyarci Deportivo La Coruna.

A kuma lokacin ne Barcelona wadda ke rike da Copa del Rey za ta karbi bakuncin Real Betis.