Labarai

Kwata Kwata Buhari Bai Fahimci Zanen Gadar Da Ganduje Ya Kai Masa Ba, Cewar Kwankwaso

Daga Comr Abba Sani Pantami
Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce sam Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai fahimci zanen gadar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kai masa ba.

A farkon makon nan ne dai Ganduje ya kai zanen wata gadar sama mai hawa uku ga Buhari a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja wacce ya kudiri aniyar ginawa a kan shatale-talen NNPC dake unguwar Hotor a birnin Kano.

Sai dai a wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC ranar Juma’a, Sanata Kwankwaso ya ce yana matukar mamakin yadda Gandujen ya ciyo bashin Naira biliyan 20 da nufin yin aikin da ya ce na Gwamnatin Tarayya ne.

Ya kuma zargi Gwamnan da gaza fahimtar hakikanin bukatar jama’ar jihar Kano, inda ya ce kamata ya yi harkar ilimi ta kasance a kan gaba ba wai gina gadar sama ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: