Daga Bello Muhammad sharada
Duka maganganun da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na siyasa ne. Abin da ya sha fada ne cewa sune ‘yan siyasa a barsu su yi siyasarsu, malamai su rike buzu da carbi, ‘yan kasuwa su rike kasuwancinsu, sarakai su rike sarautarsu.
A duk kalaman da Kwankwaso ya yi babu bakuwar magana. Ya saba, ya dade yana yi, halinsa ne kuma ba zai canza ba. Yana son ya firgita malamai masu magana ta siyasa akan mumbari. Bukatarsa su kame bakinsu, duk iya hegen dan siyasa da yaudararsa da zaluncin da zai yi, su zura ido suna kallo.
Jawo hadisai da ayoyin Alkur’ani da shirya gangamin wa’azi don baiwa Kwankwaso raddi ba shi ne amsa ba. Ni a fahimtata ba zai gane wannnan salon ba. Da yaren da ya iya za a fuskance shi.
Amsar da ta dace da Kwankwaso shi ne duk wani malami da almajiri da yake jin cewa Kwankwaso ya yi ba daidai ba, kuma ya kamata ya biya farashi akan abin da ya yi, ya gaya wa jama’arsa ta kowacce siga, duk abin da Sanata Kwankwaso ya nuna ko ya daga a siyasa ya ce a zaba a ranar Asabar wannan mai zuwa ko Asabar ta sama ko a wane mataki kada a zabe shi, a je a zabi mafi kusancin hamayya da Kwankwaso.
Kamata ya yi kowa ya huce haushinsa akan ‘yan takarar Kwankwaso. Zai fi jin zafin kayen zaben yaransa na PDP, akan zafin wa’azi da za a yi. Siyasa ya yi, siyasa ce amsa.