Labarai

Kwankwaso Ne Kadai Nagartaccen Dan Takarar Shugaban Kasa – Inji Alan waka

Kwankwaso Ne Kadai Nagartaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Yankin Arewa, Cewar Mawaki Aminu Ala

Daga Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

“Ni ba Kwankwaso ne dan takara ta na shugaban kasa ba, amma shi kadai ne mutumin da idan ya zama shugaban kasa zai dawo da martabar Arewa, duk wasu damammaki da Arewa ta rasa za ta iya samun su, kama daga ingantattun hanyoyi mota da jiragen kasa, bunkasa harkar kasuwanci da inganta harkar ilimi, da duk wani dama da Arewa ta rasa a baya”.

“Kwankwaso mutum ne maras tsoro, wanda zai iya taka tuk wanda ya yi mai gani-gani, ba tare da shakku ko tsoro ba, dan ko wannan rainin wayon da ‘yan Biafra ke yi wa mutane ba za su yi shi a mulkin Kwankwaso ba, sannan mutum ne mai tsananin son kai domin mutum ne mai kishin Nijeriya fiye da kowace kasa. Sannan ya fi son yankin Arewa fiye da kowane yanki, a Arewar ma yafi son jihar Kano, a Kanon ma ya fi son Madobi fiye da ko ina, inji mawaki Aminu Alan Waka.