Har Gobe Ina Tare Da ‘Yan Fim, Kuma Zan Ci Gaba Da Ba Su Gudummawa, Cewar Sanata Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana tare da ‘yan fim kuma zai ci gaba da ba su gudummawa don ganin sun harkar su ta kara habbaka.
Sanatan ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, a yayin ziyarar sirri da wasu daga cikin membobin kungiyar ‘yan fim na Arewa, wato ‘Arewa Film Makers Association’ suka kai masa a gidansa dake jihar Kaduna.
A yayin jin ta bakin mai magana da yawun kungiyar masu shirya finafinan na Arewa, Darakta Sanusi Oscar (4-4-2), ya bayyana cewa sun tattauna muhimman abububa da Sanatan musamman yadda gwamnatin Kano ta daurawa wasu ‘yan fim da mawaka karar tsana saboda sun nuna har yanzu suna tare da Kwankwaso. Wanda suke ganin cin zarafin da ake yi musu ba ya rasa nasaba da siyasa.
Shi ma Sanatan ya nuna rashin jin dadinsa ga yadda ake cin zarafin ‘yan fim din musamman masu masu goyon bayansa, inda ya kara da cewa har ya gama gwamnatinsa bai taba kama wani dan fim ko mawaki ba, kuma ya ba su dukkanin goyon bayan da suke bukata. Haka kuma ya kara da cewa har yanzu yana tare da su kuma zai ci gaba da ba su gudummawa.
Wasu daga cikin tawagar ‘yan fim din da suka ziyarci Kwankwason, sun hada da Baba Karami, Sanusi Oscar, Nazifi Asnanici, Mustapha Nabraska, Umar M. Sharif, Zaharadden Sani da sauransu.
Add Comment