Siyasa

Kwamitin karɓar mulki na NNPP ya zargi Ganduje da sayar wa da ɗan sa ginin ma’aikatar gwamnati

Kwamitin karɓar mulki na NNPP ya zargi Ganduje da sayar wa da ɗan sa ginin ma’aikatar gwamnati

Kwamitin karɓo karon gwamnati da aka yi sama-da-faɗi da su, ƙarƙashin babban kwamiti na karɓar mulki na jam’iyar adawa ta NNPP-, ya yi zargin cewa gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sayarwa da ɗan sa, Abba Ganduje, ginin ma’aikatar gwamnati kan ƙasa da Naira miliyan 10.

Shugaban kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan sun kai ziyara ma’aikatar, wacce ta ke da alhakin tabbatar da bin ƙa’idoji a harkar gwamnati a jiya Laraba, kamar yadda sanarwa daga kakakin zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ta bayyana yau a Kano.

Sanarwar ta ce Bichi ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin ya bankaɗo cewa an yi wa ginin ma’aikatar, wacce ke kan titin State Road kudi, Naira miliyan 500, amma sai gwamnatin Ganduje, ta sayar wa da ɗan gwamnan ginin kan ƙasa da Naira miliyan 10.

Ya kara da cewa shi kuma Abba Ganduje tuni ya sayar da ginin kan Naira miliyan 300, inda a cewar Bichi, a yau Alhamis ɗin nan da a ke shirin fara rushe ginin.

Bichi ya nuna takaicin abinda kwamitin ya bankaɗo, inda ya siffanta shi da yinwa kadarorin gwamnati ta’annati, inda ya kara da cewa “ba haka a ka zaci gwamnatin da aka baiwa dama shekaru 8 tana mulki zanta yi ba.”

Sanarwar ta ce zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinnsa za ta bi hanyoyi na shari’a wajen ganin ta kwato duk kadarorin da gwamnatin Ganduje ta yi hafzi da su.