Labarai

Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Lagos Ya Ziyarci Ɗan Okadan Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Ci Ma Zarafi A Legas 

Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Lagos Ya Ziyarci Ɗan Okadan Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Ci Ma Zarafi A Legas

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, a ranar Alhamis, ya ziyarci ɗan okadan nan Alhassan Usman , wanda wasu jami’an ‘yan sanda suka ci zarafinsa lokacin da suka ƙwace masa babur ɗinsa.

A wani fefan bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya, an ga wasu ‘yan sanda uku suna zaluntar ɗan Okadan. An ga ɗaya daga cikin ‘yan sandan yana buga sandarsa a kan matashin yayin da wani kuma ke ture shi

Matashin ya yi ƙoƙarin riƙe babur ɗinsa don hana ’yan sandan tafiya da shi, inda ya samu mummunan rauni yayin da ‘yan sandan suka lakaɗa masa duka.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan Legas, Owohunwa ya yi Allah wadai da abin da ‘yan sandan suka yi, ya kuma shaida wa jama’a cewa tuni aka ɗauki matakin ladabtarwa a kan su.

Ya ce, “CP Idowu Owohunwa a yau ya ziyarci matashin da al’amarin ya rutsa da shi, ya kuma ziyarci al’ummar Hausawa a Kasuwar Abattuwa da ke Agege.

“CP wanda ya yi Allah wadai da yadda ‘yan sanda suka yi amfani da ƙarfi fiye da ƙima wajen aiwatar da dokar hana amfani da babura a wasu sassan jihar Legas, ya tabbatar wa jama’a cewa matakin ladabtarwa da aka fara a kan ‘yan sandan. za a kai shi ga ƙarshe na ɗaukar matakin da kuma bayyana sakamakon a bainar jama’a.

Ya ce hukumar ‘yan sanda za ta ci gaba da tabbatar da cewa an bi doka, ba tare da yin ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da dokokin ƙasa.