Uncategorized

Kwalliya za ta biya kudin sabulu – Neymar

PSG ta yi nasara a kan Guingamp da ci 3-0

Dan kwallon Brazil Neymar ya ce ya yi murna da kwallon da ya ci wa Paris St-Germain a wasan farko da ya buga wa kungiyar a karawar da ta doke Guingamp. 

 

PSG ta yi nasarar doke Guingamp 3-0 a wasan makon farko a gasar Faransa, kuma Neymar wanda kungiyar ta saya mafi tsada a tarihi a bana ya ci kwallo sannan ya bayar da wadda aka zura a raga.

Neymar ya ce “Mutane na tunanin barin Barcelona da ya yi kamar karshen rayuwarsa ne, ba su san abun ba haka yake ba”.

“Na ji dadi fiye da kowanne lokaci. Na buga wasa na yi murna, kuma ban ji wani bambanci ba kamar yadda nake taka-leda”.