Nasiha

Kuskuren Dan Arewa, Daga Queen Zeeshaq

KUSKUREN DAN AREWA…

Daga Zainab Ishaq (Queen Zeeshaq)

Kullum maganar mu daya ce ana zalintar ‘yan arewa, to wai shi dan arewa yaushe zai gane kan sa ne? na dauka duk lokacin da maciji ya sare ka, in ka ga baqin tsimma gudu ka ke, don tsira da rayuwar ka? to mu arewa me yake damun tunanin mu?

Na yadda najeriya ta kowa ce, amma ai kowa da yankin da Allah ya ajje shi, me yasa ba zamu hakura mu zauna a yankunan mu, mu nemi arziqin ba?

Dan Arewa yana da kima da daraja, Idan akai duba da magabatan arewa na kwarai, wadanda sukai gwagwarmaya (misali, Ahmadu Sardauna, Tafawa Balewa da sauran su) sun nemawa arewa daraja da mutunci, duk da cewar da shugabannin mu a cikin tarwatseqar mu, amma mu kan mu muna da abinda za muyi.

Zaman lapia yana da dadi, amma kuma duk dan da ya hana uwar shi bacci to bai kamata shi ma ya rintsa ba, muna ayka sakwanni a hotuna da rubutu, shugabanni in ba su ga wani ba suna ganin wani, in ba su basu gani ba makusantan su na gani, amma sai suy shiru, ba wanda zai ce uffan, Idan ta’annatin da ake a kudu ace a arewa ake yi da tuni mun shiga 3, duk wani tsarin jefa uquba sai an samu cikin sa.

Shugabanni nan ya kamata ku san cewa Idan fa ba ku dau mataki ba lallai ga abinda zai faru…..

Yadda ‘yan kudu ke mana kawai za muyi musu

Shugabanni sun yi biris, to mu bar kai musu koken mu, in an mana a kudu, sai mu rama a arewa.

Ba sauran yadda, aminci, cinikayya ko daga qafa tsakanin mu da su.

Taimakon El-farouq jakada