Cin Hanci da Rashawa

Kungiyoyi 107 Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Kira Ga Tinubu Da Ya Tsaftace Hukumar EFCC

Kungiyoyi 107 Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Kira Ga Tinubu Da Ya Tsaftace Hukumar EFCC

 

Biyo bayan babbar zanga-zangar da hadakar Kungiyoyi masu yaki da cin hanci da rashawa suka gudanar a Lagos, karkashin jagorancin Crime and Corruption Monitors, sun ja hankalin zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan ya tsaftace hukumar EFCC daga hannun shugaban ta na yanzu Abdurrashid Bawa.

 

Jagoran zanga-zangar Idowu Bello wanda ya karanta sakon kungiyoyin hadakar ya ja hankalin gwamnati da cewa ” Idan hukumar da aka kafa don ta yaki cin hanci ta fake da neman kudi da farautar ‘yan siyasa da rashin adalci da zabarin masu laifi, da yiwa wadanda ake tuhuma tarko, hukumar ta kasa amfani da ikon ta, na yaki cin hanci da rashawa kamar yanda aka tsara a jadawalin gudanarwar ta. Anan kasa ta shiga rudani na gazawar aikin ‘ya ‘yan ta. An rawaito cewa kusan kaso tamanin na zargin cin hanci da rashawa da gangan aka ki kaisu kotu, ake gudanar da shari’oinsu a ofisoshin hukumar EFCC ba a gaban alkali a zaurukan kotu ba.

 

Ko satin da ya wuce Gwamna Matawalle na Zamfara yayi ikirarin cewa Abdurrashid Bawa shugaban hukumar EFCC ya nemi ya ba shi cin hancin dala miliyan biyu, don ya dakatar da zargin sa da hukumar ta keyi.

 

A shekarar 2019, tun kafin Abdurrashid Bawa ya zama shugaban hukumar EFCC, an taba zargin sa tare da kama shi a wata hukumar yaki da cin da rashawa inda ya saida manyan motoci a kalla 244, wanda kudin kowace daya ya kai miliyan 20 zuwa 30. Ya saida wasu ga mutanen sa N 100,000.

 

Ana kuma zargin sa da aringizon kudi har dalar Amurka dubu dari uku, 300,0000, a hotal da sauran bukatu. Kudin da sun fi karfin albashin sa. Wanda ya kashe a lokacin Umra.

 

Ana kuma zargin sa da hade kai da ministan shari’a Abubakar Malami, da saida gangunan man fetur, da gwamnatin tarayya ta rike, zargin da ya saba da 31(2) da (4) na dokar hukumar EFCC 2004. Malami da Bawa ana zargin su da saida kayan hukumar ba bisa ka’ida ba.

 

Bawa da Malami sun tabarbarar da zargin da ake yiwa tsohon gwamnan Gombe Danjuma Goje. Wanda aka share shekara bakwai ana fafatawa a kotu, rana tsaka aka samu Goje ya samu ‘yanci ba tare da sahalewar kotu ba.

 

Haka nan rikicin Abel Isa a Sokoto, wanda ake zargin jami’an hukumar sun dinga dukan sa har ya mutu. Shima kawo yanzu sun tabarbarar da zargin.

 

Masu zargin sun bukaci a gaggauta sauke Bawa daga shugabancin hukumar ta EFCC.

Kamar kowace hukumar gwamnati, akwai tsarin gudanarwa da yanda ake tafiyar da binciken shugaban da ake zargi. Wannan tsarin amsasshe ne a duniya gabadaya.

 

Magabacin Bawa a shugabancin EFCC, Ibrahim Magu ya sauka daga kan mukamin sa, biyo bayan zarge-zargen da ake masa na saba doka da karya ka’idar aiki a hukumar, daga baya bincike ya gabata, kuma an same shi da laifi.

Rashin sauke Bawa da baiwa doka dama a gabatar da bincike a kan sa, na iya haifar da raini da ganin wallen hukumar ga ‘yan kasa da sauran al’ummar duniya.

 

Fatan mu sabon zababben shugaban kasa mai jiran gado Ahmed Bola Tinubu zai daura damarar dawowa da hukumar darajar ta.

 

‘Yan kasa na cike da burin ganin anyi garan-bawul ga hukumar, wacce zata iya zama fitila da ma’unin darajar kasar nan a idon duniya