Kungiyar ‘Yan Canji Sun Koka Da Hukumar DSS Kan Kama Membobinsu Da Ta Yi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano
Kungiyar yan Kasuwan Canji na yankin Arewa sun bukaci a gaggauta sako musu mambobinsu wadanda hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ke tsare da su sama da mako biyu ba tare da wani sahihin bayanai ba ko bayyana laifin da suka aikata ba.

Cikin wasikar da kungiyar ‘yan canjin ta rubutawa Hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS dake nuna cewar, tun a ranakun 9, 10, 12 da kuma 16 na wannan wata ta Maris da hukumar ta gayyaci mambobinta su 26 daga jihohi biyar dake fadin kasar don amsa tamboyi, bayan sun amsa gayyatar ba’a sake ji daga garesu ba.

Kana babu wani daga cikin iyalansu da aka bawa damar ganawa dasu, duk da korafin da wasu daga cikin iyalen suka yi na cewar, akwai wadanda ke fama da matsalar jinya da ke bukatar kulawa ta shan magunguna akan lokaci wanda hakan wata babbar barazana ce ga lafiyarsu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 732

Lauyan dake wakiltar Kungiyar, Barista Rilwan Idris ya ya yi kari da cewa.

Kungiyar ta kara da cewar an ci zarafin mambobinta tare da take hakkinsu wajen cigaba da tsare su ba tare da bayyana laifin da suka aikata ba balle a gurfanar da su a gaban kotu, la’akari da sashi na 35 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 kamar yadda aka yi gyarar fuska.

Mai magana da yawun gamayyar Kungiyoyin Arewa a Najeriya, Abdulazeez Sulaiman, ya ce ya kamata a bi matakai da doka ta tanada don bincike saboda gudun take hakkin dan Adam. Duk da damar da doka ta baiwa wasu hukumomin tsaro a Najeriya na gudanar da bincike kan wasu laifufuka da ake zargin wani mutum, hukuma ko kungiya da aikatawa, dokar ta bayyana hanyoyi da matakai da za’a bi wajen gudanar da binciken da zimmar gano bakin zare.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: