-Advertisement-


Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Kungiyar Samarin Tijjaniyya Ta Kasa ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamna Ganduje


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abba Anwar

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta kara tabbatar da goyon bayanta ga jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sannan sun amince da cewa a kowane lokaci a shirye suke da su taimakawa tafiyar gwamnan.

Shugaban kungiyar ne Sayyadi Habibu Dan Almajiri ya bayyana haka, da su ka kai wa gwamnan wata ziyara ta musamman a ofishinsa. Ya kara da cewa alakarsu da Ganduje ba ya yau ba ce.

Sun bayyana yadda suka ba gwamnan Kano sunan Khadimul Islam, tun shekaru bakwai da su ka wuce. “Da jimawa mun ga yadda kungiyarka ta Gidauniyar Ganduje take kokari wajen musuluntar da Maguzawa da kuma kokarin da kake wajen gina Masallatu da makarantu” in ji Dan Almajiri.

Kungiyar ta yabi gwamnan wajen kulawa da su ba tun yau ba, “Mun shaida cewar yana da kokarin zuwa ofishinmu. Kuma tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu yana bibiyar ayyukan da muke yi. Hakan ya nuna mana yadda kake kokari wajen yin haba-haba da jama’a ba wulakanta Dan Adam. Ka na ganin girman kowa,” ya ce.

Dan Almajiri ya kara da cewa a wannan lokacin ne kawai a ka samu gwamnatin jihar Kano ta shiga harkar Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass, lokacin da gwamnatin ta bayar da motoci sama da guda sittin don zuwa Maulidin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 324

- Advertisement -

Ya ce a saboda haka su na tare da gwamnan a abubuwan da ya sa a gaba. Ya kara da cewa “Mu na kara godiya da yadda kake neman shawarwarin shugabanninmu irin su Sheikh Khalifa Ishaqa Rabi’u Khadimul Qur’an.”

“Mu na kuma kara nuna godiyarmu ga Mai Girma Gwamna saboda yadda yake kulawa da mutanenmu ‘yan darikar Tijjaniyya wajen nade-naden mukamai da a ka yi a gwamnati. Tun daga lokacin da ka hau kan kujerar mulki kawo yanzu,” in ji Dan Almajiri.

Bayan yabawa gwamna kan harkokin Tijjaniya, ‘yan kungiyar sun yabawa gwamnatin Ganduje wajen irin kokarin da take yi wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa. Su ka ce su ma sun tsunduma cikin harkar yaki da miyagun kwayoyi ka’in-da-na’in.

Daga bisani kuma gwamna Ganduje ya yabawa kungiyar wajen kokarinsu na ilmantar da jama’a kan harkokin addinin Musulunchi.

Saboda yabawa kuma da ya yi da ire-iren ayyukam alheri da suke yi, ya ba wa kungiyar kyautar mota mai cin mutane 36. Ya mika motar ga shugaban kungiyar Dan Almajiri, ya yi kira gare su da su yi amfani da ita wajen shiga sako-sako don aikin kungiya.

Ya kuma yi fatan zai duba abubuwan da ofishin kungiyar ta su ke nema na kujeru da ragowar kayan aiki don tabbatar da cewa sun samu yanayi mai kyau saboda ci gaba da abubuwan alheri.

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.