Labarai

Kungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa (AFMAN) Reshen Jihar Neja Ta Yi Zaben Shugabanninta

Kungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa (AFMAN) Reshen Jihar Neja Ta Yi Zaben Shugabanninta

Daga Haruna Suleiman Utono.

An yi takarar ne tsakanin Hon. M.B Muktar tare da Muhammad Kabir.

Zaben wanda aka gudanar a Youth Center Minna babban birnin jihar Neja ya samu halarta masu sa ido daga kungiyar ‘yan Jaridu na kasa reshen jihar Neja.

 

Saidai tun kafin fara zaben mafi yswa daga cikin ‘yan takara sun janyewa junansu. Idan ban da kujera daya wanda shi ma ana gab da fara zabe sai Muhammad Kabir ya janyewa Hon. M.B Muktar wanda hakan ya sa Hon. M.B Muktar ya samu darewa kan kujerar Shugabancin Kungiyar ta AFMAN ta jihar Neja.

Hajiya. Hadiza Idris Kuta wacce ta wakilci kwamishinan matasa da wasanni, ta yaba kan yanda ‘yan takarar suka janyewa junansu, wanda tace hakan ys nuna hadin kan Kungiyar.

Sabon shugaban Kungiyar na AFMAN Hon. M.B Muktar ya yabawa abokin hamayyarsa bisa ga janyewar da ya yi masa.

Hon. M.B Muktar ya sha alwashin ciyar da Kungiyar gaba tare da ganin AFMAN ta yi gogayya da sauran takwarorinta dake fadin kasar nan.

 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.