Education

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU Ta Shiga Yajin Aikin Jan Kunne Na Wata Guda

Daga Comr Abba Sani Pantami

Bayan dogon zaman da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU tayi cikin daren Litinin, majalisar zartaswar kungiyar ta amince za a tafi yajin aikin jan kunnen gwamnatin tarayya a amsa bukacinsu.

Wata majiya daga cikin ganawar cewa ASUU ta yanke wannan shawara ne don baiwa Gwamnatin Tarayya damar yin abinda ya kamata ko kma su tafi yajin aikin din-din-din.

A cewar majiyar: “Kawai muna son baiwa gwamnati dama ne don tayi abinda ya dace domin hana yajin aikin din-din-din. Mu ma fa iyaye ne kuma ‘yayanmu na karatu a jami’o’in amma ba zamu zuba ido harkar ilimi ta lalace a kasar nan ba.”

“Muna wannan gwagwarmaya ne amfanin kowa, dukkanmu zamu ji dadi ida aka gyara. Manyan masu fada aji sun sanya bak amma da alamun gwamnati bata shirya ba. Shugabanmu zai yi bayani ga yan jarida an jima.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement