Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa ASUU ta gargadi gwamnatin tarayya da na jihohi tare kuma da yin barazanar rufe dukkanin jami’o’in gwamnatin tarayya da na jihohin kan kin biyan albashin malaman da gwamnatin ta ki yi.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a karshen makon nan da muke ciki, shugaban shiyyar kungiyar ta Port Harcourt, Farfesa Beke Sese ya ce malaman jami’a ba za su ci gaba biyewa gwamnati na fakewa da batun tabarbarewar tattalin arziki suna kin biyan malaman jami’ar albashinsu ba.
“Tura ta kai mambobinmu bango ta yadda dole mu zabi shiga yajin aiki sakamakon rashin bada himma da wannan gwamnati ta ke yi kan batun hakkokinmu”
“Muna kira ga dalibai, iyaye, da ma ‘yan jarida da duk wani mai ruwa da tsaki a wannan gwamnati da ya sanya baki a wannan maganar kafin mu kai ga shiga yajin aikin sai baba ta gani a dukkan jami’o’in gwamnatocin jihohi da ta tarayya”.
Jami’o’in da ke wannan shiyya ta Port Harcourt da Farfesa Beke ke shugabanta sun hada da: jihar Ribas, jami’ar Neja Delta, Amassoma, Jami’ar jihar Bayelsa, jami’ar gwamnatin tarayya ta Otuoke, jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Ribas da jami’ar ilimi ta Ignatius Aturu da ke jihar ta Ribas.
Add Comment