Labarai

Kungiyar Izala Za Ta Yi Gagarumin Taron Bude Gidan Baki Mallakarta A Birnin Abuja

Izala Za Ta Yi Gagarumin Taron Bude Gidan Baki Mallakarta A Birnin Abuja

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar Izala tana gayyatar ‘yan uwa Musulmi zuwa wajen kaddamar da sabon gidan baki da ta gina mallakarta a birnin Tarayya Abuja.

Gidan mai kantama kantaman Falo har guda hudu, tare da dakuna 20 na alfarma, an kashe masa kudi kimanin Naira miliyan dari biyu da goma sha biyar, (N2,15,000.000.00). Kuma ansamu kudin ne ta hanyar tara fatun layya na shekara biyu kacal da ‘ya’yan kungiyar Izala sukayi a tarayyar Naijeriya, tare da tallafin Wasu Daidaku.

 

Gidan an riga da an sanya masa suna ‘Gidan Shekh Abubakar Mahmud Gumi Jibwis Guest Hous’ wanda yake unguwar Life Camp a cikin birnin Abuja. Ka na Gidan Terrace house ne Guda Hudu, kuma Ko wane block yana da suna.

An sawa ‘Block A’ Suna Alh Muhammad Musa Maigandu.

‘Block B’ Shekh Ismaila Idris.

‘Block C’ Shekh Imam Abubakar Ikara

‘Block D’ Alh Ali Ibrahim Tofa (AA Tofa)

Dan haka shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau yake gayyatar ‘ya’yan kungiyar a cikin Naijeriya da su halarci bude sabon gidan domin suga inda abun da suke taimakawa yake tafiya ba gara ba zago…

Za’a gabatar da gagarumin wa’azi mai kama da na Kasa a masallacin Helkwatar Izala dake Utako a daren asabar 12-Dhul-Qadah-1438H, 5-August-2017M bayan sallar isha’i har zuwa lokacin da ya samu insha Allah.

Za’a yi taron bude gidan Baki da Izala ta gina a ranar Lahadi 13-Dhul-Qadah-1438H, 5-August-2017. Da misalin karfe 10:00am na safe insha Allah.

Kazalika shugaban na Izala yana bada sanarwar cewa, duk wanda zaizo wajen bude sabon gida to ya Taho da gudunmawar Naira dubu daya (N1000) kacal, kuma mabiya wannan shafi namu mai albarka ba’a barku a baya ba, Kuna iya bada naku tallafin na kudi akalla Naira dubu daya, ko fiye da haka domin a ranar da za’a bude gidan baki a ranar za’a kaddamar da tubalin gina sabuwar sakateriyar Helkwatar Izala mallakar kungiyar wanda ya hada ďa gina katafaren Masallaci, Katafaren Asibiti katafaren dakin taro da kataren office a birnin Abuja insha Allah.

Tabbas tunda muka iya gina wannan gida a shekara biyu to zamu iya gina wannan sakateriya cikin kankanin lokaci insha Allah.
Kuma ana gayyatar kowa da kowa, musamman wanda ya samu iko domin shaida akan abun da ake gabatarwa.

Sai kunzo………

 

Souce In Rariya

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.