Rundunar sojin saman Najeriya ta ce wasu ‘yan Boko Haram sun kai wa wani jirginta mai saukar ungulu hari a lokacin da yake kai ma’aikatan lafiya garin Gwoza na Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
A wata sanarwa da kakakinta, Guruf Kyaftin Ayodele Famuyiwa, ya sanya wa hannu, rundunar ta ce mayakan na Boko Haram sun yi harbe-harbe a kan jirgin kirar Mi-17, amma kuma ba wanda ya rasa ransa ko da yake matukin jirgin ya yi rauni.
Jirgin saman mai saukar ungulu dai ya tashi ne daga Maiduguri don kai ma’aikatan wadanda ke gudanar da wani shiri na kwanaki biyu na taimaka wa marasa lafiya a garin na Gwoza.
Sanarwar ta kara da cewa duk da raunin da ya yi, matukin jirgin ya kai ma’aikatan inda ya nufa domin ganin shirin ya ci gaba na tare da wani tsaiko ba, sannan ya koma masauki.
Bayan harin, a cewar rundunar, an tashi wani jirgin saman yaki da kuma wani jirgin mai saukar ungulu dauke da manyan bidigogi zuwa yankin, wanda ke tsakanin Bama da Gwoza domin kawar da maharan.
Rundunar ta kuma ce rahotannin sirri daga dakarun sojin ƙasa su tabbatar cewa an kashe ‘yan Boko Haram din, lamarin da ke nuna cewa an yi nasara a harin da aka kai.
Ba wannan ba ne dai karo na farko da Boko Haram ke yi wa sojojin Najeriya kwanton bauna, duk kuwa da ikirarin da hukumomi ke yi cewa an karya lagon mayakan kungiyar.
Add Comment