Labarai

Kuna Ganin Na’urar Magance Satar Shanu Za Ta Yi Tasiri A Nijeriya?

Satan shanu na daya daga cikin matsalolin da ya dade yana ciwa al-umman da hukumomi kasar Nijeriya tuwo a kwarya.
Hakan yasa kwararru suka bullo da wata sabuwar dubara da za’a rika amfani da wata na’urar fasaha wajen tantance dabbobin tare da gano wadanda aka sace.
A yanzu haka an kaddamar da tsarin a jihar Kaduna bayan nazari da masana kimiyya da likitocin dabbobi, da masana harkar tsaro, tare kuma da kwararru a harkar sadarwa suka yi na tsawon shekaru.
Malam Ibrahim Maigari Ahmadu, daya daga cikin jagorar, ya ce za’a rika sanyawa dabba wni karamin na’ura wanda bai wuce girma kwayar shinkafa ba mai lambobi a cikinta, za’a yi amfani da allura wajen sanya wa a cikin jikin dabba.
Malam Ibrahim ya kuma ce duk dabbar da aka sanyawa na’urar za’a iya gano ta a duk lokacin da aka sace ta.
Kungiyoyin Fulani makiyaya na kasar Nijeriya sun bayyana gamsuwar su da bullo da wannan fasaha, inda suka ce za ta yi matukar taimakawa wajen magance satar shanu da a kai kasar.
Ga hotunar irin na’urar a kasa

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.