Kun san yaushe za a fara shari’ar Zakzaky a Kaduna?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An sake gurfanar da shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta ‘yan Shi’a (IMN) Sheikh Ibrahim el-Zakzaky a gaban wata babbar kotu da ke jihar Kaduna ranar Laraba.

Wannan ne karon farko da Sheikh El-Zakzaky ya bayyana a gaban kotun tun bayan kisan da aka yi wa magoya bayansa lokacin arangamar da suka yi da jami’an tsaro a Abuja, babban birnin Najeriya.

Talla

Sojoji sun ce mutum uku ne suka mutu a yamutsin da aka yi a makon jiya, ko da yake ‘yan Shi’a da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International sun ce fiye da mutum 40 aka kashe.

Gwamnatin jihar Kaduna na tuhumarsa da kisan wani soja lokacin wani rikici da magoya bayansa suka yi da sojoji a garin Zariya a shekarar 2015.

Sai dai Sheikh Zakzaky ya musanta zargin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Janairu na 2019.

An yi tsammanin za a bayar da belin Malamin amma hakan ba ta samu ba.

A zaman kotun na wata Mayu, lauyan da ke kare Zakzaky Barista Maxwell Kenyon ya nemi kotun ta ba da belinsa, sai dai alkalin kotun ya yi watsi da bukatar.

Mai Shari’a Kurada ya nemi lauyan a kan ya gabatar da bukatar neman belin a rubuce.

Lauyan masu shigar da kara Daris Bayero ya bukaci kotun ta amince wa hukumar tsaro ta DSS ta ci gaba da tsare jagoran a hannunta.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: