-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Kun San Abin Da Atiku Ya Fi Sha’awa?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana jerin abubuwan da ya fi sha’awa a duniya.

Ya bayyana haka ne ta hanyar maudu’in #AskAtikuYourself, wanda ke nufin #KuTambayiAtikuDaKanku.

Abubuwan da aka tambaye shi wadanda kuma ya bayar da amsarsu su ne:

  • Wanne kulob din kwallon kafa ka fi sha’awa?
  • Wanne abinci ka fi sha’awa?
  • Wacce waka ko kida ka fi sha’awa?
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Da yake bayar da amsa, dan takarar na PDP ya ce “Arsenal ne kulob din kwallon kafar da na fi sha’awa.”

Ya kara da cewa babu abincin da ya fi kauna kamar shinkafa dafa-duka, yana mai cewa wakokin marigayi Fela Kuti su ne wakokin da ya fi kauna da sha’awar sauraro.

Atiku Abubakar ya ce lokacin da Fela ke raye, yana yawan halartar wuraren da yake waka.

Sai dai ya ce a yanzu babu mawakin da ya fi kaunar sauraren wakokinsa kamar Davido.

Ranar 16 ga watan nan na Fabrairu ne za a gudanar da zaben shugaban Najeriya, inda Atiku Abubakar zai fafata da Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke son yin wa’adi na biyu a kan mulki.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: