-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Kudi Ya Kawo Farraka Tsakanin Mawaka Da Fadar Shugaban Kasa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga shafi’u Ibrahim Abuja

Kudi masu gida rana, bayan lashe zaben shugaban kasa muhammadu Buhari, gamayyar mawakan hausa da masu shirya fina finan na hausa sun kai wata ziyarar taya murna ga shagaban a fadarsa dake binnin taraiya Abuja.

Amma daga bisani sai wani cece kuce ya barke tsakanin “yan fadar ta shugaban kasa da masu sana’ar ta waka a dai dai lokacin da suka kammala ziyarar kuma fadar ta kawomusu dan abin sallama wato abinda ake kira na goro ko muce na mota.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

- Advertisement -

Sai dai Kawo wadannan kuda de baiyiwa wasu daga cikin masu wannan ziyara dadi ba domin kuwa suna ganin sunfi karfin irin kudin da fadar ta kawomusu, nan take sai hayaniya ta barke a tsakanin su wasu daga ciki sukace bazasu karbi kudin da aka kawo ba domin suna ganin sunyi kadan.

nan take wanda ya kawo kudin abin ya bashi mamaki da haushi ya bude baki ya tambayi mawakan cewa ba kunce domin Allah kuke san shugaba Buhari ba ba domin kudi ba? amma yanzu zan kawo muku kudi wuri na gugar wuri har naira 250,000, wasu daga cikin ku kuma naira 100,000, wasu kuma naira 50,000 amma ku raina? bayan kuwa mawakan da masu sana’ar ta flim sun saba kai irin wannan ziyara da mutane kamar 80 wasu lokutan 50, amma wannan karin sai suka dunguma harda yaran aikinsu inda saka kai ziyarar da mutane 180 kuma kowa ya samu irin wannan kudi, wannan abu ya batawa manzon kawo wannan kudi rai.

tambayarmu a anan shine mawaka da ‘yan flim ne kawai suka zabi wannan gwamnati?

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: