Labarai

‘Ku Rike Mukamin Ku Ina Tare Da Gwamna Bala’

Honarabul Dayyibu Chiroma yana cikin jerin sunayen mutane da Ministan ilimin Nijeriya Malam Adamu Adamu ya ba su mukami, inda aka tura shi ‘𝐹𝑒𝑑𝑒𝑟𝑎𝑙 𝑃𝑜𝑙𝑦𝑡𝑒𝑐ℎ𝑛𝑖𝑐 𝑆ℎ𝑎𝑛𝑑𝑎𝑚 𝑗𝑖ℎ𝑎𝑟 𝑃𝑙𝑎𝑡𝑒𝑎𝑢’.

Bayan fitowar sunan sa Hon Dayyibu ya ki amincewa da wannan dama da aka ba shi, inda ya yi godiya ga ministan tare da bayyana sha’awar sa na cigaba da aiki da Gwamnatin jihar Bauchi karkashin Gwamna Bala Muhammad.

Honarabul Dayyabu ya ce ya fi sha’awar cigaba da bayar da gudummawar sa karkashin Gwamna Bala. Maimakon haka ya bukaci ministan ya mika mukamin ga wasu da ba su samu ba.

Yanzu haka dai Honarabul Dayyibu Chiroma yana aiki da Gwamnatin jihar Bauchi a matsayin shugaban Hukumar Lura da rarraba magunguna na jihar Bauchi karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: