Daga Jamilu El Hussain Pambegua
Tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi II ya yi kira ga daukacin Malaman jihar Kano da su ajiye Banmance bambancen ra’ayi domin marawa gwamnatin Kano baya domin rushe da’awar Sheikh Abduljabar.
Sarkin Kanon ya yabawa Gwamnatin Kano kan yadda ta yi gaggawar shigowa lamarin kafin da’awar Malamin ta yi nisa cikin al’umma.
An dai yi zargin Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya bullo da wata da’awa wacce ta sabawa dokokin jihar Kano, wanda tuni Malaman addini Musulmci daga sassan Jihar suka soki da’awar Malamin.