Ku Guji Siyan Wayoyin Hannu Wajen Wadanda Baku Sani Ba – Rundunar ‘Yan Sanda

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Babban jami’in ‘yan sanda na rundunar ‘yan sanda dake Ilaro, SP Oni Waheed, ya gargadi al’umma da a kiyayi siyan wayar hannu wajen mutanen da ba sansu ba, saboda gujewa fadawa cikin matsala da doka, dalilin yawaitar sace-sacen waya da ya yi kamari.

Jami’in ya yi wannan gargadin ne a yayin da yake ganawa da manema labarai, yau Alhamis a garin Ota na jihar Ogun, ya ce maimakon haka mutane su dinga siyan wayoyin hannu a shagunan da aka san na siyar da wayar ne, saboda kaucewa shiga matsala da doka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta…

1 of 661

‘Yanzu ana iya bibiyar wayoyin hannu cikin sauki, in aka saci waya aka siyarwa mutum za a iya bibiyarta, in kuma aka bibiya to za a kama wanda aka same shi da wayar a hannu, in mutum a hannun wanda bai sani ba ya siya, ya shiga matsala kenan, saboda jami’an ‘yan sanda zasu kama wanda suka samu ne da waya a hannun shi.’

Talla

Inji SP Waheed Jami’in ya koka da yadda sace-sacen waya ya yi kamari, har ta kai ana iya hallaka mutum don kawai a kwace mishi wayar shi, sannan barayin suna siyar da wayoyin da suka yi fashin su ne mafi yawan lokuta ga mutanen da basu ji ba ba su gani ba, inda suke fakewa da cewa wata muhimmiyar bukata ce ta taso musu, amma a kashin gaskiya masu laifi ne, a haka suke jefa mutane cikin halin ha ula’i.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: