Labarai

Ku Dawo Min Da Kudi Na, Kyauta Ne Aka Bani – Andrew Yakubu Ga Kotu

Tsohon shugaban hukumar mai ta kasa NNPC, Andrew Yakubu ya bukaci kotu da ta mayar masa da kudaden sa da ta mika wa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC. 
Yakubu ya na magana ne akan kudaden nan, dala miliyan 9.8 da fam dubu 74 da hukumar ta samu a gidan sa da ke Kaduna a kwana kwanan nan.
Ta hannun lauyan sa Ahmed Raji, Yakubu ya shigar da kara da ke bukatar babbar kotun tarayya da ke zama a Kano da ta janye umarnin da ta bayar na mika kudaden sa ga gwamnatin tarayya.
Karar ta bayyana cewa kotun ba ta hurumin mika kudaden ga gwamnati saboda ba a jahar Kano ya aikata laifin da ake zargin sa da shi ba.
Haka kuma takardar karar ta bayyana cewa karya dokar da ke karkashin sashi na 28 da 29 na hukumar EFCC ne kadai ya ke bukatar kwace kudaden wani ba karya wata dokar daban ba.