Ku Daina Bari Wasu na Rinjayar Ku Wajen Yada Rahotanni Masu Haifar Da Nakasu Ga Ci Gaban Kasa -Buhari Ya Gargadi `Yan Jarida

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shawarci shugabanni da kuma mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, da suka kasance akan yada sahihan rahotanni a ko da yaushe tare da gargadin su akan illolin rahotanni na bogi da shaci fadi.

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya gargadi ‘yan jarida da su daina bari wasu miyagun mutane na rinjayar su wajen yada rahotanni masu cin karo da akidu na zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.

Talla

Shugaban kasar ya yi kiran ne yayin karbar bakuncin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, NUJ, Nigerian Union of Journalists, bisa jagorancin shugaban ta, Mista Chris Isiguzo, da suka ziyarci fadar sa ta Villa da ke garin Abuja a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

Buhari ya gargadin na neman kawo karshe tare da badda annobar yaduwar rahotanni na bogi a fadin kasar nan masu haifar da barazana ta zaman lafiya gami a kawo nakasun ci gaban kasa ta kowace fuska.

Kiran na da muhimmanci a halin yanzu kamar yadda shugaban kasa Buhari ya zayyana sakamakon yadda rayuka da dama suka salwanta baya ga asarar dukiya mai tarin yawa a sanadiyar yaduwar rahotanni na bogi.

Ya nemi kungiyar ta ‘yan jarida da su hada gwiwa tare da gwamnatin sa wajen bunkasar ci gaban Najeriya tare da inganta alakar ta da sauran kasashen duniya yayin fafutikar kawo karshen annobar yaduwar rahotanni na bogi.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: