Siyasa

Kotun sauraron ƙarar zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya za ta fara zama a wannan rana

Kotun sauraron ƙarar zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya za ta fara zama a wannan rana

 

A wannan rana ne kotun sauraron ƙarar zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya, za ta fara sauraron ƙarar da dan takarar jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim (AA Zaura) ya shigar a gaban ta, yana kalubalantar nasarar dan takarar NNPP, Sanata Rufai Sani Hanga, tare da neman kotun ta kwace nasarar Hanga ta dawo masa da ita, domin Hanga yaci zaɓe ne ta hanyar magudi, kuma ba’a bi ƙa’idar zaɓe ba wajen zaɓen da ya bawa NNPP nasara, kamar yadda lauyan AA Zaura mai suna Barista Ishaka Dikko, ya bayyana.

 

Sai dai lauyan dake kare Sanata Hanga da NNPP, Barista Meshak Ikpe, ya ce a shirye suke tsaf domin gabatar da hujjoji da kuma shaidu da zasu tabbatar da nasarar jam’iyyar NNPP a zaɓen Sanata na shekarar 2023, kamar yadda shima lauyan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, Barista Abbas Haladu, ya ce shaidu biyu kacal zasu gabatarwa kotu domin tabbatar da sakamakon da suka fitar, kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito.

 

AA Zaura ya fadawa kotu cewa zai bukaci wanda zai rika fassara masa abubuwan da ake fada daga Ingilishi zuwa Hausa, yayin sauran wadanda ake ƙara ba su bukaci tafita ba.

 

Malam Ibrahim Shekarau na cikin wadanda ake ƙara a wannan Shari’a.

 

#NasaraRadio

#AmanarTalaka

24/5/2023