Siyasa

Kotun Koli ta tabbatar da takarar Abba Kabir Yusuf

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halattaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano a zaben da ya gabata.

Alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al’amin (Little) na cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba.

Kotun ta ce Little, wanda ya yi nasara a kotun farko a Kano, ba shi da hurumin shigar da kara kan zaben da bai shiga ba.

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba gida-gida”, ya sha kayi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.

Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe suka musanta.

A yanzu haka dai jam’iyyar PDP da dan takararta sun shigar da kara a kotun saurarar kararrakin zabe inda suke kalubalantar nasarar ta Gwamna Ganduje.

Wannan hukunci ya kawo karshen takaddamar da aka dade ana yi kan halaccin zaben fitar da gwannin da jam’iyyar PDP ta yi a Kano.
Masu lura da al’amura na ganin zai kuma bawa jam’iyyar PDP da magoya bayanta damar mayar da hankali kan shari’ar da suka shigar ta zaben na watan Maris.

A yanzu haka dai kotun na ci gaba da zama, amma ba a kai ga yanke hukunci ba tukunna.
A fakaice hukuncin ya kuma tabbatar da matakan da bangaren Kwankwasiyya na jam’iyyra ta PDP ya dauka a lokutan zaben fitar da gwanin, wanda shi ma ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar ta Kano.