Kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar gwamnati tarayya a kan jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.
Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.
[ads1]Alkalan sun ce an dawo da shi Najeriya ne ba bisa ƙa’ida ba.
Sannan sun ce gwamnatin tarayya ta gaza faɗar wajen da ta kama Kanu duk da manya-manyan zarge-zargen da take yi masa.
Kotu ta ƙara da cewa shirun da gwamnatin ta yi na nuna cewa ta yarda da abin da Kanu ya ce cewa sato shi aka yi aka dawo da shi Najeriya da ƙarfi.
Kotun ta ce tsare Kanu da yi masa shari’a a kowace kotu karya doka ne tun da ba bisa ƙa’ida aka mayar da shi Najeriya ba.
[ads1]Da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan Kanu kuma ɗan rajin kare hakkin ɗan adam, Ifeanyi Ejiofor, ya rubuta a shafinsa Facebook a ranar Alhamis cewa, “a ƙarshe dai Kanu ya yi nasara.
“An ba da damar ɗaukaka ƙara, an saki tare da wanke Oyendu Mazi Nnamdi KANU. Mun yi nasara!, ya rubuta.
Wasu labaran da za ku so ku karantaWannan hukunci ya zo ne bayan da babban lauyansa Mike Ozekhome, ya yi ta roƙon kotu ta yi watsi da sauran tuhume-tuhume bakwai da Babbar Kotun Tarayya ke shari’arsu bayan ta yi watsi da takwas daga cikin tuhuma 15 da ake masa tun farko.
Tun da fari, Mai Shari’a Jummai Hannatu Saki ta soke buƙatar da masu shigar da ƙara suka yi ta neman a gaggauta yin shari’ar, saboda tasowar wasu abubuwan.
[ads1]Ta kuma ajiye batun ba da belin Nnamdi Kanu a gefe guda, har sai an ji hukuncin Kotun Daukaka ƙara.
Gwamnatin Najeriya tana tuhumar Nnamdi Kanu da laifuka 15 da suka haɗa da na ta’addanci da cin amanar ƙasa da neman assasa ƙungiyar IPOB da ke son ɓallewa daga ƙasar.
Amma a watan Mayun 2022, Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya ta cire wasu tuhume-tuhumen takwas daga cikin 15.
Sannan Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da batun bayar da belin Nnamdi Kanun.
Mai Shari’a Binta ta bayyana buƙatar bayar da belin a matsayin “saɓa ƙa’idojin shari’a.”
Add Comment