Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Maryam Sanda


0 166

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babbar kotun Abuja, mai zama a yankin Maitama tayi watsi da Bukatar da Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta, ta shigar gaban ta, inda take bukatar kotun ta kori karar da aka shigar gabanta, yau Alhamis kotun ta yi watsi da wannan bukatar.

Mai shari’a Yusuf Halilu, ya bayyana cewa daga dukkan shaidun da wadanda ake kara suka shigar gaban kotun, shaidun sun tabbatar sa cewa dole wadanda ake karar su kare kansu, sannan suna bukatar kara gabatarwa da kotun karin shaidu, don haka ba zai yiwu ayi watsi da wannan karar ba.

‘Bukatar da Maryam Sanda ta shigarwa kotun, na ayi watsi da sauraron wannan karar da ake yi, ba zai yiwu ayi watsi da sauraron wannan karar ba, don haka ina umartar da ta kare kanta a gaban kotu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

’ inji Alkalin In ba a manta ba, ana tuhumar Maryam Sanda ne bisa zargin ta da kashe mijinta Bilyaminu dan tsohon ciyaman din jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Muhammad.

Sannan kotun ta wanke tare da sakin mahaifiyar Maryam, Maimuna Aliyu, dan uwanta Aliyu Sanda, da mai aikin gidansu Sadiya Aminu, wanda dukkansu ake zargin su da taimakawa Maryam wajen kashe mijinta nata, ta hanyar kawar da hujjojin kisan.

Alkalin ya ce ‘yan sanda masu shigar da kara basu gabatarwa da kotu gamsassun hujjojin da zasu tabbatarwa da kotun laifin da suke zargin mutanen da aikatawa ba, don haka kotun ta sallami mutanen uku, sannan ta wanke su fes daga tuhumar da ake musu. An dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Mayu da zamu shiga.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.