Kotu ta yankewa kansila hukuncin zaman gidan kaso na wata uku


0 151

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wata kotu a jihar Gombe ta yankewa wani kansila hukuncin zaman gidan yari na wata uku sakamakon samun sa da laifin sayen kuri’a.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato EFCC ce gurfanar dashi gaban kotu bayan ta zarge shi da aikata laifin a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da ya gudana.

Hukumar EFCC ta ce ta damke kansilan mai suna Ishiyaku Garba a rumfar zabe mai lamba 007 da ke mazabar Bolari inda ta rutsa shi yana raba kudi a rumfar zaben.

Ishiyaku Abubakar wanda kansila ne a mazabar Bolari ta gabas a jihar Gombe ya amsa laifin da ake zarginsa bayan alkalin kotun ya karanto masa jerin laifuffukan da ake zarginsa da su.

A lokacin zaman kotun, lauya mai kare kansilan ya roki kotun da ta sassautawa wanda ake zargin wajen yanke masa hukunci.

Kotun dai ta samu kansilan da laifuffuka uku inda ta yanke mashi hukuncin zaman gidan yari na wata uku ko kuma ya biya tarar naira 295,000.

Sayen kuri’a lokacin zabe

An dade ana kokawa kan batun sayen kuri’a a Najeriya wanda ya zama ruwan dare a lokacin zabubbuka.

A lokacin da aka gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na gwamnoni a Najeriya, hukumar EFCC ta wallafa hotuna da dama daga wurare daban-daban kan yadda ake sayen kuri’a ko kuma hotunan makudan kudi da ake niyyar rabawa masu zabe.

Me doka ta ce kan sayen kuri’a?

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati na EFCC da ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun bayyana sayen kuri’a a matsayin laifin cin hanci.

Ko a wani taron wayar da kai da ICPC ta gudanar a watan Disambar 2018 ta ce sayen kuri’a zamba ce a dimokradiyya.

A wancan lokacin shugaban hukumar ya shawarci ‘yan Najeriya da su guji biyewa marasa kishin kasa masu yaudararsu da kudi ko abun masarufi.

“Idan har ku ka bar su suka yi nasara ta hanyar yin hakan, to kuwa za su tabbatar sun sace dukiyarku da aka ware don samar da ruwan sha da inganta harkar lafiya da ilimi da gina tituna idan har suka hau,” a cewarsa.

Mece ce illar sayen kuri’ar talakawa?

Malam Kabiru Sufi wani mai sharhi ne kan al’amuran siyasa a Najeriya kuma Malami a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano ya bayyana cewa babbar illar da ke tattare da sayen kuri’un ita ce nakasta dimokradiyya.

“Babu wata dimokradiyya da za ta samu ci gaban da ya dace idan dai har za a dinga amfani da halin tsanani da mutane ke ciki ana kara tauye hakkinsu ta hanyar sayen kuri’unsu don an san ba su da mafita sai yin hakan,’ in ji Sufi.

Illa ta biyu kuwa ita ce sayen kuri’u na iya sauya sakamakon zaben gaba daya.

Malam Sufi ya ce a lokaci daya sai a sauya zukatan mutane da akidarsu wajen tursasa su su zabi wanda da farko ba shi suka yi niyya ba, don kawai an ba su kudi.

“Wani lokacin ma har hakan na sauya hasashen da tun farko aka yi cewa ga wanda alamu suka nuna zai ci, amma lokaci daya sai lamari ya sauya,” a cewar Sufi.

Sannan wata babbar illar ita ce hakan zai sa ba za a dinga samun wakilci da shugabanci na gari ba, don kuwa duk masu fitar da kudi su sayi kuri’a to fa ana ganin lallai za su yi abun da duk za su iya don ganin sun ci riba a kudin da suka kashe ba ma mayar da uwar kudin ba kawai.

Ko ma dai mene be, lallai batun sayen kuri’u ba abu ne mai alfanu ga Najeriya da jama’arta ba, kuma ba abun da za ta yi sai nakasta kasar da kara durkusar da ita.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.