Kotu ta umurci ‘yan sanda su bayar da belin mawaƙin da ya Mari ɗan sanda Seun Kuti bayan sa’o’i 48
Kotun majistare da ke zamanta a Yaba, Legas, ta umarci ‘yan sanda da su tsare Seun Kuti,
na tsawon sa’o’i 48 domin gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin daya daga cikin jami’anta.
An gurfanar da mawakin a gaban kotu a ranar Talata da yamma inda aka tuhume shi da laifin cin zarafin wani dan sanda.
Laifin ya sabawa sashe na 356 na dokar laifuka ta Najeriya.
S.A Adebese, dan sanda mai gabatar da kara, ya roki kotun da ta cigaba da tsare wanda ake kara tsawon kwanaki 21, har zuwa lokacin da za a ba shi shawarar lauyoyi daga hukumar da ke sauraron kararrakin jama’a (DPP).
Lauyan mawakin, Femi Falana, ya roki kotu da kada ta tsare wanda yake karewa.
Babban alkalin kotun, Adeola Olatunbosun, ya amince da bukatar ‘yan sanda na ci gaba da tsare mawakin amma sai da karin sa’o’i 48.
Alkalin kotun ya kuma yanke hukuncin cewa ‘yan sanda su kammala bincike cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da bayar da belin Kuti.
An kama mawakin ne da sanyin safiyar ranar Litinin kuma an tsare shi a sashin binciken laifuka na jihar (SCID) wanda aka fi sani da Panti.
An kama Seun ne bayan an dauki hotonsa yana cin zarafin wani dan sanda a kan gadar Third Mainland,dake Legas.
Wani ɗan gajeren faifan bidiyo da ya bazu a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda ya nuna Kuti, sanye da jar riga da farar wando, yana ture ɗan sandan, wanda ya tsaya kusa da wata motar ‘yan sandan Toyota Hilux.
Daga nan sai mawakin ya ci gaba da marin jami’in yana ihu, “Kai ka yi hauka, ka yi hauka?”
A cewar Kuti.
Add Comment