KannywoodLabarai

Kotu Ta Sallami Naziru Sarkin Waka Bayan Yane mi Afuwar Ganduje

Wata kotun majistare a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sallami shari’ar da take yi wa Naziru M. Ahmed wanda aka fi sani da sarkin waƙa bayan ya nemi afuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun, wadda mai shari’a Aminu Gabari yake jagoranta, ta sallami shari’ar da take yi wa sarkin waƙa ne bisa laifin fitar da wata waƙa kafin hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ta.

Hakan ne ya sa a watan Satumban 2019 aka kama Naziru Sarkin Waƙa amma daga bisani kotun majistaren ta sake shi bayan ya cika sharuɗan belin da kotun ta yanka masa.

Sai dai a farkon watan jiya kotun ta soke belin da aka bai Naziru Ahmed inda ta gindaya masa wasu sababbin sharuɗan belin.

Daga nan ne ta aike da shi gidan yari saboda rashin cika sharuɗan a kan lokaci, duk da cewa an gindaya sharuɗan ne a ƙurarren lokaci, a cewarsa.

Me ya faru a kotun?

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan gwamnatin jihar Kano, Barrister Wada Ahmad Wada ya gabatar da wata takardar bayar da haƙuri ga gwamnatin Kano wadda ya ce daga hannun Naziru M. Ahmed ta fito.

A cikin takardar, wadda Sarkin Waƙa ya rubuta ta zuwa ga Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, ya ce “ni Naziru M. Ahmed ina bayar da haƙuri matuka bisa zargin da aka yi mini kuma ina da-na-sanin abin da hakan ya haifar.”

Mawaƙin ya ƙara da cewa ya bayar da haƙurin ne bayan masu ruwa da tsaki sun tsoma baki a cikin lamarin.

Lauyan Naziru M. Ahmed, Barrister Sadik Sabo Kurawa, ya ce sun cimma wannan matsaya ce sakamakon fahimtar junan da aka samu daga ɓangarorin biyu.

“Abin da ya faru a yau shi ne da ma an samu daidaituwa tsakanin bangaren gwamnati da na wanda ake ƙara, shi ya sa suka zo yau suka kawo ƙarshen tuhume-tuhumen da ake yi masa suka wanke shi daga ciki,” in ji shi.Daga nan ne Mai Shari’a Aminu Gabari ya sallami Naziru M. Ahmed sannan aka rufe shari’ar baki ɗaya.

Naziru M. Ahmed shi ne sarkin waƙar tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II wanda ya daɗe yana kai ruwa rana da Gwamna Ganduje har sai da aka cire shi daga kan mulki a watan Maris da ya gabata.

An sha zargin gwamnatin jihar Kano da yin amfani da hukumar tace fina-finai ta jihar wajen gallaza wa ‘yan fim da kuma mawaƙan Kannywood da suke goyon bayan masu adawa da ita.

A baya, an zargi hukumar, wadda Isma’ila Na’abba Afakallah yake jagoranta, ta yi ta takun-saƙa da wasu ‘yan fim irin su Sani Danja, Sanusi Oscar da makamantan su waɗanda ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne ɓangren tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, mutumin da gwamnan Kano ke matuƙar adawa da shi.

Sulaiman Lawan

Sulaiman Lawan Usman is a graduate in Bsc Mechanical engineering from Kano University of Science and Technology, Wudil. Also a founding member of ArewaBlog. And now he is working with Vision FM Nigeria as Head of engineering

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: