Kotu Ta Mallakawa Gwamnatin Tarayya Kadarorin Tsohuwar Minista Madueke Kimanin Naira Bilyan 14
Wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Nijeriya kaddarorin tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke, da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.
Kotun ta mallaka wa Nijeriya wani katafaren gidan Ms Diezani da ke yankin Banana Island da ke Lagos, wanda kudinsa ya kai $37.5m, kimanin naira biliyan 13.
Haka zalika, mai shari’a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin tarayya naira sama da naira miliyan 84 da kuma sama da dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.
A kwanan baya dai kotun ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kadarorin na wucen gadi, bayan hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta nemi kotun ta mallawaka wa gwamnati kadarorin.
Bayan haka ne dai kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a kafafen yada labarai, domin duk wanda ke da wani dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na din-din-din ba ya kawo dalilinsa gaban kotun.
A zaman da aka yi ranar Litinin, lauywan EFCC, Anselem Ozioko, ya shaida wa kotun cewar hukumar ta yi biyayya ga hukuncin kotun.
An tuhumi Diezani kan maguɗin zabe
Ya ce duk da cewar an mika wa masu hannu da tsaki a lamarin hukuncin kotun na bai wa gwamantin damar kwace kadarar, babu wanda ya bayyana a kotun domin daukar kalubalantar umarnin na kotun na kwace kadarar.
A rashin dalilin ne kotun ta mallaka wa gwamantin Najeriya kadarorin da din-din-din.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka kwace kadarorin tsohuwar ministar man.
A watan Afrilun 2016, EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai naira miliyan 593 daga hannun tsohuwar ministar.
Ana zargin ta da sace wa da kuma yin facaka da kudin kasar a lokacin da take ministar man, ko da yake ta sha musanta zargin.
A watan Fabrairun 2017 ma, wata babbar kotun tarayya a Nijeriya ta amince a halatta tare da mallakawa gwamnatin kasar kudaden da aka samu daga wajen tsohuwar ministar man, Diezani Allison-Madueke.
Add Comment