Labarai

Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Daga Abubakar Abba
Babbar Kotun Tarayya da ke da zaman ta a Babban Birinin Tarayyar Abuja, ta dakatar da ‘yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara bisa yunkurinsu na tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Mahdi Gusau.

An ruwaito cewa, yan majalisar sun kitsa shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Mahdi Gusau wanda ya ki bin gwamnan jihar zuwa koma wa jamiyyar (APC), bayan gwamnan Jihar Bello Matawalle tare da yan majalisun dokokin jihar da sauran yan majalisun wakilai da ke wakiktar jihar a tarayya sun fice daga jamiyyar (PDP).

‘Yan kwanaki biyu bayan gwamnan jihar ya canza sheka zuwa APC, mataimakin gwamnan ya gudanar da gangami a jihar tare da magoya bayansa na jamiyyar sa ta PDP.

Hakan ya harzuka, yan Majalisar dokokin jihar Zamfara, inda suka bukaci da ya gurfana a gaban Majalisar domin yin gangamin na siyasa a jihar duk da cewa, ‘yan bindiga na ci gaba da hallaka mutane a jihar.

Amma bisa hukuncin da alkali mai shari’a na kotun ta tarayya Obiora Egwuatu ya yanke, ya bayyana cewa, ‘yan Majalisar ba su da ikon tsige Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Mahdi Gusau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: