A jiya ne kotun jiha mai lamba 18 dake zamanta a Ungoggo karkashin mai shari’a Zuwaira Yusuf, ta cigaba da sauraron shari’ar jarumar finafinan Hausa na Kannywood, Hafsat Idris, wacce aka fi sani da Hafsa Barauniya, da wani kamfani mai suna UK Entertainment ya shigar da kara bisa yadda yace sunyi yarjejeniyar aikin TV Show na Naira Miliyan daya da dubu dari uku, amma kafin a karasa aikin ta gudu.
Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, kamfanin ya bukaci kotu tasa Hafsa ta dawo musu da wadancan kudade, sannan kuma ta biya su kudin diyya Naira Miliyan goma, dukda cewa wacce ake karar bata halarci zaman kotun ba, saidai ta turo da wakilci na lauyanta, Umar Garba Kabara, amma dai kotu ta dage cigaba da sauraron wannan kara zuwa lokaci na gaba, kamar yadda wakilin Dala FM, Abubakar Sabo ya rawaito.
A baya dai lokacin da aka fara sauraron wannan shari’a, wacce ake kara Hafsat Idris, bata halarci zaman kotun ba, kuma bata turo da wakilci ba, amma yanzu lauyanta yazo kotu kuma ya gabatar da takardunsu na martani ko kuma kariya ga bangaren da yake wakilta, kafin daga bisani kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Disamba mai zuwa, domin gabatar da shaidu na dukkan bangarori.
Daga: Kano Online News
11/11/2021
Add Comment