Kotu ta bada belin Rochas Okorocha kan naira miliyan 500

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

Wata Kotun Tarayya a Abuja ta bada belin Sanata Rochas Okorocha kan naira miliyan 500 da gabatar da mutum guda da zai tsaya masa.

Jaridar Punch ta rawaito Alkalin Kotun, Inyang Ekwo na cewa bada belin zabi ne na kotu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 904

Sannan a cewar jaridar, alkali Ekwo ya ce wanda zai tsayawa Okorocha a belin dole ya kasance ya na da kadarori a inda ake zaman kotun, kuma dole ya bada jinginar takardun filin nasa.

Sannan alkalin ya bukaci sanatan ya bada fasfo dinsa na tafiya, a kuma sanar da hukumar shige da fice matsayar kotun.

Ya kuma umarci ka da Sanata Rochas ya kuskura ya bar kasar ba tare da izinin kotu ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.