Kotu ta aike da matar da ake zargi da yunƙurin kisan ƙaramar yarinya gidan gyaran hali
Kotun majistiret mai lamba 39 dake zamanta a unguwar Gyaɗi-gyaɗi, ƙarƙashin mai Shari’a Mustapha Hassan, ta yi umarnin a tisa ƙeyar matar nan da ake zargin ta cakawa ƙaramar yarinyar nan mai suna Sharifa Usman ƴar unguwar Gadan Ƙaya Wuƙa a ciki wadda har yanzu ke asibiti, domin samun kulawar likitoci.
Matar mai suna Fatima Salisu mai kimanin shekaru 35, an yi zargin ta ɗauki ƙaramar yarinyar daga unguwar Gadan Ƙaya, inda ta kai ta garin Mariri, a ƙaramar hukumar Kumbotso wanda aka zargin a can ne tayi amfani da Wuƙa ta caka mata a gefen cikinta har sai da ta fito ta ɗaya gefen.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, bayan fitowa daga kotun, ya zanta da Fatima Salisu da ake zargi da yunƙurin kisan kai, wanda ta nuna nadamar abinda ta aikata.
Add Comment