Labarai

An kori ‘yan sanda uku daga aiki ko me suka aikata?

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa ta kori wasu jami’an ta uku, a bisa dalilin kage da sharrin da su ka yi wa wani matashi, har su ka raba shi da naira 200,000.00.

Rundunar ta bayyana haka ne a ranar Litinin din yau, inda ta bayyana sunayen Sufeto Okelue Nkemeonye, Sajan Braimoh Sunday da kuma Sajan Yusuf Olukoga.

Dukkan jami’an ‘yan sandan sun a aiki ne a “Area N’’, da ke Ijede-Ikorodu, Lagos. An dai kore su ne bayan da aka yi musu shari’ar-cikin-gida a Babbar Shiyya ta ‘’Zone Two da ke Onikan-Yaba.

An samu wadannan ‘yan sanda da laifin fakewa bakin banki rike da bindigogi, sai da suka bari wani matashi da ya kammala aikin bautar kasa ya fito daga banki, su ka yi caraf su ka cafke shi, su ka yi masa sharrin cewa wai shi dan “yahoo yahoo ne, wato masu damfarar mutane ta intanet.

A karshe sun yi ta karbar kudi har sai da suka karbi naira 200,000.00. dama kuma an aiki yaron ne a cikin bankin domin ya aika da kudi naira 200,000.00 ga asusun ajiyar wani mutum.

Binciken da ‘yan sanda su ka gudanar ya nuna cewa ‘yan sandan sun yi karya, sun ce su ma’aikatan rundunar zaratan ‘yan sandan kai-daukin-gaggawa ne, wasu SARS, alhali kuma karya su ke yi.

Tuni dai Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris ya jinjina wa yaron saboda yadda ya fito ya bayyana zalincin da ‘yan sandan su ka yi masa.

Ya kara da cewa duk wani korafi da aka kai wa hukumar dangane da wani dan sanda, to za a yi gaggawar daukar matakin hukunci, domin rundunar sa ta kudiri aniyar aiki a kan tafarkin kawo canji a kasar nan.

Rundunar ‘yan sanda dai ta kuma bayar da wadannan lambobi da ke kasa cewa idan jama’a sun a da wani korafi a kan ‘yan sanda, to gaggauta tuntubar wadannan lambobi:

08057000001: A kira wannan lambar.
08057000002: A kira wannan lambar.
08057000003 A tura sakon WhatsApp a wannan lambar.