Kokarin da shafin sada zumunta da muhawara na Facebook ke yi na yaki da yada labaran bogi ya fuskanci babban koma baya, bayan da wasu Kamfanoni biyu masu taimaka masa suka janye daga bai wa shafin taimakon tantace gaskiyar labari.
Kamfanin dillancin labarai na AP da shafin Snopes, sun ce sun janye daga aiki da Facebook saboda kudaden da ake basu bai taka kara ya karya ba.
Facebook dai ya dage tukuru wajen dakile yadda ake yada labaran karya ko marar sahihanci ta shafin, bayan caccakar da ya fuskanta a kan rawar da ya taka a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka a shekara ta 2016.
- Advertisement -
Sai dai masu bincike na cewa ba wani sauyi aka samu na a zo a gani ba.
Har yanzu dai kamfanin ya ce nauyi ne daya rataya a wuyansa na yaki da labaran bogi da taimakon masu tantace sahihin bayanai daga waje.