Ko Me Yasa Ronaldo Yake Neman Jan Hankalin Messi Zuwa Italiya?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya kalubalanci Lionel Messi ya bar Barcelona ya dawo wani kulub na Italiya.

Dan wasan na Portugal ya koma taka leda a Seria A a kungiyar Juventus daga Real Madrid kan fam miliyan 99.2.

Talla

An dade ana kallon Ronaldo da Messi a matsayin gwarzayen ‘yan wasan duniya, inda dukkaninsu suka lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, kafin Modric ya lashe kyautar a bana.

“Zan so ya zo Italiya wata rana,” in ji Ronaldo mai shekara 33.

“Ina fatan zai amince da wannan kalubalen, amma idan yana jin dadi a inda yake, ina girmama hakan.”

Talla

Ronaldo ya shafe kaka tara a Real Madrid bayan ya baro Manchester United a 2009, yayin da kuma abokin hamayyarsa Messi ya shafe rayuwarsa a Barcelona.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

“Da aka tambayi Ronaldo ko yana kewar Messi, sai ya ce: “aa, ai shi ne yake kewa ta.”

“Na buga wasa a Ingila da Spain da Italiya da Portugal da kuma tawagar kasa ta, amma Messi har yanzu yana Spain.”

“Kila ya fi bukata ta. Ni a waje na, na dauki rayuwa kalubale, ina son haka kuma ina son na dinga faranta wa mutane rai.”

“Dan wasa ne mai kyau, amma ban rasa komi ba a nan. Wannan ce sabuwar rayuwa ta.”

Na karbi wannan kalubalen a Italiya kuma komi na tafiya daidai, na nuna har yanzu ni dan kwallo ne.”

#BBCHAUSA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: