Ko Me Yasa Pogba Yakeso Neymar Ya Koma Mancherster

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan wasan tsakiyar kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya ce yana fatan wata rana zai buga wasa a kungiya daya da dan wasan PSG, Neymar saboda a cewar Pogba Neymar babban dan wasa ne wanda kowa yake son zama tare dashi.

Neymar ya yabi kwazon dan wasa Pogba a shekara biyu da suka wuce, inda ya ce salon wasan dan kwallon tawagar Faransa zai da ce da buga wasa a Barcelona wanda hakan yasa aka fara rade radin cewa barcelona din zasu nemi Pogba.

Talla

Sai dai kuma yana yi ya sauya inda ba za su iya wasa tare a Barcelona ba, bayan da Neymar ya koma Paris St-Germain a kakar shekarar data ganata shi kuwa Pogba ya bar Jubentus a watan Agustan shekara ta 2016, inda ya sake komawa Manchester United da buga wasa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

Pogba na fatan wata rana zai buga wasa da Neymar, ya kuma ce yana tuna abinda dan kwallon Brazil din ya fada a kanshi, zai so ya yi wasa tare da shi musamman a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Ya kuma kara da cewar ‘’A Brazil kwallon kafa ita ce rayuwa, kowa yana buga kwallon kafa, yana jin dadin kallon yadda yake buga wasa, yana da dabaru, ya lakanci kwallon kafa, sannan ya iya buga wasa, yana jin dadin kallon yadda yake buga kwallo.

#Hausaleadership

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: