Labarai

Ko Kunsan Saura Kwana Biyu Suka Rage (2) A Rife Rigista a Shafin Npower

Gwamnan jihar Kaduna yayi kira ga marasa aikin yi a jihar dasu yi rajistan N-Power

– Ana sa rana za’a kulle rajistan a ranar 27 ga watan Yuli

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana ma marasa aikin yi a jihar Kaduna cewa za’a rufe rajistan wannan tsarin sharbar romon dimukradiyya wato N-Power nan bada dadewa ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya bukacin mazauna jihar da basu da aikin yi dasu tabbata sun yi rajista da wannan tsarin kafin ranar 27 ga watan Yulin da muke ciki.

El-Rufai ya ja kunnen marasa aikin yi musamman dasu daure sun yi rajistan kafin wannan rana, domin kuwa a ranar ne ake tunanin kulle rajistan bayan an kwashe sama da watanni 2 ana yinsa.

Arewablog.com ta ruwaito a karkashin wannan tsari na N-Power, gwamnatin tarayya zata baiwa yan Najeriya marasa aikin yi su 350,000 aikin yi na wucin gadi na tsawon watanni 24, inda za’a dinga biyansu albashin N30,000 a duk wata.

Da fari, an dauki matasa su 300,000 a tashin farko a cikin wannan tsarin, kimanin shekara guda daya gabata kenan, kuma da dama daga cikinsu suna cin moriyar abin a yanzu haka.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.