-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Ko Kunsan Mai Jam`iyyar APC Ta Maida EFCC Kan Jiga-jigan PDP?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jam’iyyar APC ta mayar da hukumar EFCC tamkar wani tarkon Barazanar neman jiga-jigan PDP su sauya sheka ko a ka masu,

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP kamar su Godswill Akpabio da Musliu Obanikoro shine don jam’iyyar na neman ta shi mutuncin su da garfin gwmamnati.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

” Tun da gwamnati ta kyalla ta hango irin kudaden da wadannan mutane suka mallaka a asusun ajiyar su na banki sai suka yi amfani da EFCC suka fara bibiyan su sau da kafa. Daga nan sai suka rika ce musu ko su dawo jam’iyyar APC a yafe musu ko kuma su ci gaba da zama a PDP ayi musu tonon silili sannan a daure su.

Ku kalli Shari’ar Saraki kawai ya isa ku gane babu wani yaki da rashawa da ake yi kawai barazana akeyi ma Abokan hamayya zaran sun nemi wani abu Saraki yaki Yarda, sai su koma kotu su ce a Dawo da shari’ar sa, idan an daidai kuma sai shari’ar ta lafa, wannan karara ya nuna cewa APC barazana take ma yan Adawa bawai tana neman gyara bane,

Kuma yanzu Gwamnatin APC cike take fal-fal da yan Rashawa,

Lamido ya ce wannan shine ainihin dalilin da ya sa mutane kamar su Akpabio da Obanikoro suka ga ba za su iya jurewa cin mutuncin ba suka fice daga PDP din.

” Jam’iyyar APC ta yi amfani da bakin talauci da ta saka ‘yan Najeriya a ciki tana bin abokanan adawar tana bugewa da karfin tsiya. Ko kuma ka dawo jam’iyyar APC a yafe maka.

Wannan maganganu dai Lamido yayi su ne da yake bada jawabi a filin taron kaddamar da kamfen din jam’iyyar PDP a jihar Jigawa.

Bayannan ya roki wadanda suka canja sheka, wato suka fice daga PDP zuwa APC a dan kwanakinnan da su dawo jam’iyyar PDP.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: